Connect with us

Labarai

Kwastom Ta Cafke Wasu Haramtattun Kayayyaki Na Sama Da Miliyan 800

Sashin ayyuka na tarayya, FOU, shiyyar A na hukumar kwastam ta Kasa, NCS, sun kama motoci da kuma tayoyin da aka yi amfani da su wanda kudin su ya kai Naira miliyan 813.

Jami’an sun kama mutane 12 da ake zargi da shigo da wadannan haramtattun kayayyaki cikin kasar nan.

Sashin ya kuma kwato zunzurutun kudi har Naira miliyan 81.4 da aka yi ta hanyar tantancewa da bayar da sanarwar Bukatar, D/Ns, kan rashin biyan harajin kayayyakin da aka kwato daga tashoshin ruwan kasar.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Ikeja, Mukaddashin Konturola na sashin, Hussein Kehinde Ejibunu, ya ce: “An kama mutane 91 a cikin watan Agusta,sannan kuma an kama mutane 12 da ake zargi da hannu a wasu abubuwan.”

Da yake ba da cikakken bayani game da kamun, Ejibunu ya ce sun kama: “Buhuna 6,911 mai nauyin (kilogram 50kg) na shinkafar waje (fiye da lodin tirela 11), kilogiram 345 na tabar wiwi, katan 486 na kayayyakin kaji daskararre, tayoyi 368 da aka yi amfani da su. Motocin da aka yi amfani da su 13 na (tokunbo), katan 32 na batir da wa’adin su suka kare, kwantena daya mai tsawon kafa 40, Toyota Corolla daya da akayi amfani da ita, sassan mota guda 49, tayoyin mota guda 552 da aka yi amfani da su, tayoyin manyan motoci guda 205, tayoyin babur guda 32. Bales 292 na tufafin da aka yi amfani da su da kuma lita 13,529 na PMS duk suna cikin kamun da aka yi.”

Da yake kokawa kan halin rashin kishin kasa na wasu ‘yan kasuwa maza da mata ‘yan Najeriya, Ejibunu ya bayyana cewa: “Abin bakin ciki ne a lura cewa wasu ‘yan Najeriya za su biya dukkan kudaden harajin da ake biya ga hukumomin Kwastam na wasu kasashen da suke shigo da wadannan kayayyaki daga kasashen waje yayin da suke kokarin kaucewa irin wadannan kudaden a cikin asusun gwamnatin tarayyar Najeriya.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet