Labarai
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Motoci Dauke Da Albarusai Da Wiwi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu motoci guda biyu dauke da alburusai 7,500 masu rai da sinkin tabar wiwi wanda kudinsu ya haura Naira miliyan 600.
Kamfanin dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa daya daga cikin motocin ta taho ne daga Ghana ta hanyar Togo da Jamhuriyar Benin zuwa Najeriya.
Sannan mota ta biyu ta taso daga jamhuriyar Benin zuwa Najeriya, inda ta tsallake wasu shingayen binciken jami’an tsaro daban-daban.
Da yake yiwa manema labarai karin haske game da lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Nafi’u Abubakar, ya bayyana kamen a matsayin “babban lamari.”
Ya ce, a ranar 10 ga watan Satumba da karfe 7:30 na yamma, tawagar ‘yan sanda da ke sintiri a kan titin Saransa-Maje, cikin karamar hukumar Bagudo, ta kama wata babbar mota kirar kwantena mai lamba Legas IT 21520 LA, dauke da sinki-sinki 4,927 da ake kyautata zaton tabar wiwi ne akan sama da kudi Naira miliyan 300.
Abubakar ya ce an kama mutane uku Emmanuel Chukwuma daga jihar Abia, Kanta Bisa daga Ghana, da Shola Adeyemi daga jihar Ondo, yayin da wasu suka tsere.
Bayan kwana biyu, a ranar 12 ga watan Satumba, da misalin karfe 9:30 na dare, tawagar jami’an tsaron kan iyaka ta kama wata babbar motar daukar kaya mai lamba IT 21608 LA, tana dauke da harsashi 7,500 masu rai da busassun ganyen tabar wiwi guda 4,106.
“Kayan ya kai sama da Naira miliyan 300, kuma an kama wani AbdurRasaq Agbola na yankin Iyana Ajiya a Ibadan, Jihar Oyo,” in ji kakakin ‘yan sandan Kebbi.
