Connect with us

Labarai

Wata ‘Yar Kasuwa Ta Gurfana A Kotu Bisa Zargin Zuba Yajin Akan Makociyarta

 

Rundunar ‘yan sandan a ranar Litinin din nan ta gurfanar da wata ‘yar kasuwa mai shekaru 27, Mary Jideobi, a gaban wata kotun mai daraja ta daya da ke zamanta a garin Kado, a Abuja bisa zargin ta da zubawa makociyarta dakakken barkono.

Ana tuhumar Jideobi, wanda ke zaune a kauyen Tudun-Wada, a Abuja da laifin kai hari da gangan da kuma haddasa munanan raunuka.

Lauyan masu shigar da kara, Mista Stanley Nwafoaku, ya shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Janet Odeh, ta kai karar a ofishin ‘yan sanda na Lugbe.

Nwafoaku ta ce wadda ake kara a wani lokaci a watan Yuli ta gana da mai karar a lokacin da take tare da diyarta inda ta zarge su da tattaunawa a kanta.

Ya kara da cewa ba wai wadda ake tuhumar ya tsoma baki a tattaunawar da mai shigar da kara da diyarta ba, ta ce wacce ake kara ta kuma gaggayawa mai karar magana da baki.

Mai gabatar da kara ya kuma ce wadda ake tuhumar ta kara da zuba yajin barkono a kan wadda ta kai karar.

Laifin ya ci karo da tanadin sashe na 399 da na 247 na dokar Penal Code.” Inji mai gabatar da kara

Sai dai wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Malam Muhammed Wakili, ya shigar da karar wadda ake tuhumar da bayar da belinta a kan kudi naira 100,000 da kuma mutum daya da zai tsaya mata.

Ya kuma umurci wanda zai tsaya mata ya bayar da fasfo, duk wata hanya ta tantancewa da kuma bayanan BVN daga bankinsa.

Ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 19 ga watan Oktoba, domin ci gaba da sauraren karar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet