Connect with us

Labarai

Yadda Aka Tashi Daga Ganawar Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba Tare Da Cimma Matsaya Ba

Dangane da ganawar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta Kasa NLC, a ranar Litinin.

Taron dai ya kare ne ba tare da cimma mtsaba ba wanda ya gudana ranar Litinin.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong ne ya kira taron wanda ya kasa magance ko daya daga cikin batutuwan da kungiyar NLC ta gabatar.

Sai dai ministan ya bayyana fatansa na ganin an shawo kan lamarin da ma’aikatan Najeriya suka gabatar.

Ya ce Gwamnatin tarayya za ta magance matsalolin kafin karewar wa’adin da suka bayar.

“Dole ne mu gane hakikanin matsalar tattalin arzikin da ke fuskantarmu.

“Yayin da muke magance matsalolin ma’aikatanmu, dole ne mu lura da daidaiton da ke inganta ci gaban tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai dorewa ga al’ummarmu.

“A yau, ina kira ga kowannen ku da ya hada hannu wajen tattaunawa mai cike da rudani mai ma’ana, wanda zai ba mu damar dinke duk wani gibi da zai iya kasancewa tsakanin muradun ma’aikata da kuma babbar manufar ciyar da tattalin arzikin kasa gaba,” inji shi.

Shugaban NLC, Ajaero ya ce: “A cikin wa’adin da muka bayar kuma a cikin kudurin NEC, an bayyana batun NURTW a fili kuma a lokacin ne batun bai lalace ba kamar yadda yake a yanzu.

“A kan sauran batutuwa za ku ga cewa babu wata yarjejeniya kan kowa, babu CNG a ko’ina kuma matatun mai ba sa aiki, haka ma gas.

“Babu wani abu da aka yi a kan batun bayar da albashin ma’aikata da musayar kudi ko kuma batun ASUU. Duk da haka, mun yi imanin cewa daga yanzu zuwa ‘yan kwanaki masu zuwa, lokacin da wa’adin ya kare, wani abu zai faru.”

Ajaero ya ce babu gudu babu ja da baya kan yajin aikin da aka shirya na tsawon lokaci idan har ba a samu ci gaba ba kafin cikar wa’adin kungiyar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet