Connect with us

Labarai

Kananan Hukumomi 39 Ake Zargin Mutane 5800 Sun Kamu Da Mashako A Kano – UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a ranar Talata, ya ce jihar Kano ta samu mutane 5,800 da ake zargin sun kamu da cutar Mashako daga watan Janairu zuwa yau.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu rahoton bullar cutar a kananan hukumomi 39 na jihar.

Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Mohammned-Farah, ta bayyana hakan a Kano yayin wani taron wayar da kan manema labarai na kwana daya kan barkewar cutar ta Mashako.

A cewarsa, jihar Kano ce ta fi kowacce yawan masu dauke da cutar a fadin kasar nan, inda ya kara da cewa cutar mashako cuta ce mai saurin yaduwa kuma mai illa da ake iya mutuwa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Mohammned-Farah ta jaddada cewa ya zama dole a dauki matakan da suka dace don dakile barkewar cutar.

“A ‘yan kwanakin nan, mun ga karuwar masu kamuwa da cutar Mashako a Najeriya, kuma a halin yanzu Najeriya na fuskantar bullar cutar da ya kamata a dakatar da ita.

“Tun daga watan Yuli, cutar mashako na karuwa. Ya zuwa makon da ya gabata, an samu rahoton mutane sama da 400 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane 11 a Kano.

“A cikin kananan hukumomi 39 da lamarin ya shafa, takwas ne suka fi fama da cutar, ciki har da Ungogo mai mutane 2,651; Dala 989, Fagge 943, Gwale 714, Kumbotso 713, Nassarawa 538, karamar hukumar birni 506 da Tarauni 269,” inji shi.

Ya ce kashi 60.8 cikin 100 na wadanda ake zargin sun kamu da cutar yara ne da ba a yi musu alluran rigakafi ba, wanda hakan ya kara da cewa akwai bukatar a magance matsalar yaduwar musamman a jihar Kano.

“UNICEF ta kai alluran rigakafin cutar guda miliyan 1.2 ga gwamnatin jihar Kano a ci gaba da tallafa wa gwamnati game da barkewar cutar Mashako.

“Barkewar cutar Mashako barazana ce ga rayuwar yara, lafiya da walwalar yara. UNICEF na hada kai da gwamnati da abokan hulda domin daukar matakan gaggawa don ceto rayukan yaran da abin ya shafa.

“A jihar Kano, UNICEF ta tallafa wa aikin rigakafin cutar Tetanus-Diphtheria a watan Fabrairu, Afrilu, da Agusta, inda ta yi wa yara 23,200 allurar a zagaye na farko.

“Yayin da yara 277,796 suka samu allurar a zagaye na biyu da kuma wasu 29,500 a zagaye na 3 na atisayen.

“Mun dauki nauyin shugabannin gargajiya 150 game da barkewar cutar Mashako da rarraba kayan aikin IEC tare da tura VCM 1,500 zuwa kananan hukumomin da abin ya fi shafa don gudanar da wayar da kan jama’a gida-gida tare da mika wadanda ake zargi zuwa cibiyoyin lafiya.

“Kafofin watsa labarai suna da muhimmiyar rawar da za su taka musamman wajen rigakafin kamuwa da cuta, da kuma haɗarin yaduwa a cikin al’umma,” in ji shi.

Jaridar Kakaki ta rawaito cewa, Shima da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Kano Dr Muhammad Nasir-Mahmoud yace gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakai domin dakile yaduwar cutar.

“Mun himmatu wajen wayar da kan jama’a game da abubuwan da ke faruwa kuma Hukumar Yaki da Cututtuka masu yaduwa ta Kasa (NCDC) ta yi alkawarin baiwa Kano fifiko wajen rabon alluran rigakafin,” inji shi.

A yayin da yake bayyana kafafen yada labarai a matsayin abokan hadin gwiwa a yakin da ake yi da cutar ta Mashako, Nasir-Mahmoud ya bukace su da su goyi bayan wayar da kai kan yaki da cutar. (NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet