Labarai
Na Zama Dan Siyasa Ne Bisa Tsautsayi — Inji Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
Tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ya zama dan siyasa ne bisa tsautayi.
Tsohon shugaban kasar na mulkin soja ya ce bai taba son shiga siyasa ba.
Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wata kungiyar matasa karkashin kungiyar Africa for Africa Youth Initiative (A4A), a dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL) da ke Abeokuta.
Ya ce, “Ban taba son zama dan siyasa ba, na zama ne bisa bazata, amma son jama’a, son kasata ya sa na zama wani abu da na shigo ciki”.
Tsohon shugaban kasar yace Don haka, dole ne ‘yan siyasa su yi burin shiga siyasa don hidimtawa al’umma.
