Labarai
An Tsinci Gawar Wata Dalibar jami’a Da Ta Bata A Abuja
An tsinci gawar wata dalibar Jami’ar Najeriya, NOUN, Blessing Karami, wadda aka bayyana batan ta a ranar 11 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ya tabbatar wa DAILY POST hakan a ranar Alhamis.
Ta ce an gano gawar matashiyar ne a wani daji da ke yankin Karimo na babban birnin kasar.
A cewar ‘yan sanda, an kai rahoton bacewar dalibar mai shekaru 26 ga hukuma a ranar 14 ga Satumba, 2023.
PPRO ta ce kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, CP Haruna G. Garba ya bayar da umarnin gudanar da kwakkwaran bincike kan “al’amuran da suka dabaibaye Blessing Karami Moses har ya kai ga mutuwar ta.
Ta kuma bayyana cewa, jajircewar da hukumar ta yi kan lamarin kisan gilla ne, kuma ta kuduri aniyar gano musabbabin faruwar lamarin nan take.
Ta ce a halin yanzu rundunar tana aiki tare da hukumar kare muhalli ta Abuja, AEPB domin kwato gawar da ta lalace.
“Za mu ci gaba da samar da bayanai ga jama’a yayin da bincikenmu ke ci gaba da tafiya.
“Tunanin mu yana tare da iyalai da masoyan Blessing Karami Moses a wannan mawuyacin lokaci”, in ji PPRO.
