Connect with us

Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Gusau Da Ke Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani adadi mai yawa na daliban Jami’ar Tarayya Gusau da ke Jihar Zamfara da sanyin safiyar Juma’ar nan.

Wani dan kauyen Sabon Gida mai suna Abubakar Sani, ya shaida wa jaridar PUNCH cewa ‘yan bindigar da ke da yawan gaske sun kai farmaki a gidajen daliban da ke kauyen.

Ya ce daliban da aka sace yawancinsu mata ne.

Sani ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki yankin ne da misalin karfe 4:00 na asubahin ranar Juma’a, inda suka kai hari a gidajen kwanan dalibai uku.

Ya ce, “Da yawa daga cikin daliban da aka sace mata ne, yayin da sauran daliban suka tsere zuwa wani daji”.

A cewar Sani, ‘yan bindigar sun sace daliban jami’ar ne kawai amma ba su yi awon gaba da wani mazaunin kauyen ba.

Ya ce, “Lokacin da suka isa ƙauyen, sai suka tafi kai tsaye zuwa ga ɗaliban [a wajen harabar jami’a] suka fara harbi ba kakkautawa”.

“Daga baya sun kutsa cikin harabar jami’o’in sun kwaso dalibai da dama wadanda galibinsu mata ne”.

Hukumar jami’ar da kuma rundunar ‘yan sandan jihar duk sun ki cewa komai kan lamarin kawo yanzu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet