Connect with us

Labarai

Amurka Ta Gargadi Amurkawa Mazauna Nigeria Da Su Guji Shiga Wasu Jihohi 18

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta shawarci Amurkawa da su sake yin la’akari yayin balaguron zuwa Najeriya “saboda rashin tsaro, ta’addanci, tashin hankalin jama’a, garkuwa da mutane, da kuma gungun masu dauke da makamai.”

Wannan ya biyo bayan wasu shawarwarin tafiye-tafiyen da aka fitar a ranar Laraba, ta hannu ma’aikatar harkokin wajen Amurkan.

Amurka ta lura cewa wasu yankuna “suna kara samun al’amuran haɗari” saboda matsalar rashin tsaro.

Ta shawarci ‘yan kasarta da su guji zuwa jihohin da suka hadar da Borno, Yobe, Kogi, da kuma arewacin Adamawa saboda ta’addanci da garkuwa da mutane.

Saura Jihohin su ne Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, da Zamfara saboda satar mutane.

Shawarar ta kara da cewa Jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo, da Ribas (ban da Fatakwal) saboda aikata laifuka, garkuwa da mutane, da gungun masu ta’ammali da makamai.

Ya kuma kara da cewa, “ Aikata mummunan laifuka kamar fashi da makami, kai hari, satar motoci, garkuwa da mutane, da fyade ya zama ruwan dare a fadin kasar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbetholiganbetmarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetcasibomcasibomcasibomholiganbetholiganbetjojobetjojobet girişjojobet güncel girişjojobet güncel girişgrandpashabetholiganbetholiganbetgrandpashabetcasinolevantimajbetsekabetholiganbetholiganbet girişcasibomcasibom girişjojobetjojobet girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabetcasibomcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetmatbetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobetjojobet