Connect with us

Labarai

Gwamnan Kebbi Ya Bayar Da Tallafin N2m Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Kwale-kwale Ya Shafa

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya jajantawa al’ummar garin Suru da ke karamar hukumar Suru bisa hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a ranar Asabar.

Idris, wanda ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, Hakimin Suru da karamar hukumar, ya kuma bayar da gudummawar Naira miliyan biyu, inda kowane ahali suka samu N500,000.

Da yake jajantawa jama’a a ofishin hakimin garin Suru a ranar Litinin, gwamnan ya bukace su da su amince da abin da ya faru cikin aminci kuma ya yi addu’ar Allah Ta’ala ya jikan marigayan ya sada su da Jannatul Firdaus.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamitin kwamishinonin jihohi uku da wasu manyan jami’an gwamnati a karkashin kwamishinan ayyuka na musamman, Zayyanu Aliero, ya bukace su da su tabbatar da yadda aka raba tallafin.

Kamfanin dillacin laibarai na Kasa ya rawaito cewa sauran kwamishinonin biyu sun hada da Muhammadu Hamidu-Jarkuka, (Ayyukan jin kai da samar da ayyuka) da Usman Abubakar-Ladan, (Kasuwanci da Masana’antu).

Idris ya ce gwamnatinsa na matukar kishin duk wani abu da ya shafi al’ummar Kebbi, ya ce, “Don haka ne gwamnati ta mayar da al’adar ziyartar kowace al’umma idan wani abin farin ciki ko bakin ciki ya faru.

A nasa jawabin kwamishinan harkokin jin kai da wayar da kan jama’a ya ce “Muna nan a madadin gwamnatin jihar Kebbi domin jajanta muku.

“Muna nan kuma don mika ta’aziyyarmu. Allah (SWT) ya gafarta wa mamatan ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makomarsu.

“Wannan shaida ce cewa gwamna yana tare da jama’arsa kuma yana da muradin al’ummarsa a cikin zuciyarsa kuma shi ya sa yake nuna damuwa a duk lokacin da farin ciki ko bakin ciki ya faru.”

Shugaban karamar hukumar Suru, Muhammad Lawal-Suru, ya yabawa tawagar da suka kai ziyarar ta’aziyya da kuma abin da ya bayyana a matsayin mayar da martani cikin gaggawa.

Ya kuma godewa gwamnatin jihar musamman kan yadda ta tsaya tare da jama’a a lokacin da suke cikin bakin ciki, inda ya kara da cewa, “Mun yi ta tattaunawa da ku ta wayar tarho muna sanar da ku halin da ake ciki. Wannan abin yabawa ne matuka.”

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Da yake mayar da martani, Hakimin Suru, Muhammad Bello, ya yabawa gwamnan bisa yadda yake kula da al’ummarsa, inda ya bada tabbacin goyon bayan gwamnatin sa.

Ya kuma bada tabbacin cewa za’a raba kudaden ga iyalan wadanda abin ya shafa cikin adalci domin a samu saukin asarar da suka yi.
NAN

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. abrir uma conta na binance

    08/03/2024 at 6:23 am

    Your article helped me a lot, is there any more related content? Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet