Labarai
Gwamnatin Tarayya Za Ta Bunkasa Fannin Yawon Bude Ido Na Najeriya
Ministar kula da yawon bude ido, Lola Ade-John ta ce gwamnatin tarayya na shirin kirkirowa tare da inganta kayayyakin yawon bude ido na Najeriya a kasashen waje da kuma cikin gida.
Da take jawabi a Abuja 2023 ranar yawon bude ido ta duniya mai taken Yawon shakatawa da zuba jari, Ministar ta ce yawon shakatawa aiki ne mai yawa kuma suna da mahimmanci ga samar da kudaden shiga ga kasa.
Ta kara da cewa, akwai damar yin tunani a kan hanyoyin da za a kara ba da gudummawar yawon bude ido wajen cimma buri mai dorewa nan da 2030 wanda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a shekarar 2015.
A cewar Ministar, yawon bude ido ga al’umma da kuma baje kolin boyayyun duwatsu masu daraja na kauyuka a dukkan yankuna na kasarmu masu ban sha’awa da bambance-bambance, shi ne jigon samar da yawon bude ido a Najeriya.
Lola Ade-John ta bayyana muhimman abubuwan ci gaba da bunkasa harkokin yawon bude ido a Najeriya kamar; karfafawa al’umma, haɗin gwiwa da ci gaban yawon shakatawa mai dorewa, saka hannun jari a makamashi da canjin dijital.
A cewarta, duk waɗannan suna da ikon kawo sauyi kuma suna da gagarumin tasiri ga al’ummarmu.
Ministar ta sake nanata cewa kayayyakin yawon bude ido na bukatar isassun abubuwan ci gaban jama’a, kulawa da kuma ingantawa.
Ta bayyana cewa akwai kalubale da dama da ke addabar ma’aikatar amma a hankali gwamnati za ta shawo kan kalubalen cikin sauri da nasara tare da goyon baya da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabi tun da farko a wajen taron, Babban sakatare na yawon bude ido na Majalisar Dinkin Duniya, Zurab Pololikashvili, ya bayyana yawon bude ido a matsayin ginshikin tattalin arziki. Yana taka muhimmiyar rawa a cikin al’ummominmu da kuma cikin rayuwarmu gaba ɗaya.
