Lafiya
UNICEF Ta Shawarci Najeriya Kan Muhimmancin Yin Allurar Rigakafin Mashako
Yayin da cutar Mashako ta yi barkewa mafi muni a tarihin duniya na baya-bayan nan, Asusun Tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya yana kara bada shawara game da bukatar gaggawar yin allurar rigakafi.
Ya zuwa yanzu dai cutar ta shafi mutane 11,587 da ake zargin sun kamu da ita, yayin da 7,202 suka kamu da cutar a kananan hukumomi 105 a jihohi 17 har da babban birnin tarayya, wanda akasari yara ne.
Adadin wadanda suka mutu ya kai 453 a cikin wadanda aka tabbatar, wanda ke nuna adadin wadanda suka mutu ya kai kashi 6.3 cikin dari.
Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar dai yara ne ‘yan tsakanin shekaru hudu zuwa 15 wadanda ba su samu ko da kashi daya na maganin alurar riga kafi ba, lamarin da ya bayyana yanayin rigakafin a Najeriya.
UNICEF a wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar nan ta ce tana bayar da tallafin gaggawa ga gwamnatin Najeriya a kokarinta na yaki da barkewar cutar.
“Wani muhimmin bangare na wannan tallafin ya hada da siyan alluran rigakafi don tallafawa martanin gwamnati. Ya zuwa yanzu, a madadin gwamnati, UNICEF ta tura alluran rigakafin mashako miliyan 9.3 zuwa jihohin da abin ya shafa da suka hada da Kano, Bauchi, Borno, Yobe, Katsina, Kaduna, da Jigawa.
“Daga cikin wadannan allurai miliyan hudu an aika zuwa Kano, cibiyar barkewar annobar. An sayo wasu alluran rigakafi miliyan hudu kuma za a mika su ga gwamnati nan da makonni masu zuwa,” in ji sanarwar a wani bangare.
Ta kara da cewa, domin mayar da martanin yadda ya kamata kan barkewar cutar, UNICEF a Najeriya ta ce tana bukatar karin dala miliyan 3.3 nan da karshen shekara.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Wakilin UNICEF, Dr. Rownak Khan ya lura cewa “mummunan tasirin cutar Mashako babban tunatarwa ne na mahimmancin rigakafin. Najeriya na da yara miliyan 2.2 da ba su samu ko da kashi daya na allurar rigakafin ba.
“Dole ne mu hada kai mu dauki matakan gaggawa don rage wannan adadi sosai. Kowane yaro ya cancanci kariya daga cututtukan da za a iya rigakafin su. Wannan ba abin tattaunawa ba ne.
UNICEF a Najeriya ta yi kira ga abokan hulda, masu ruwa da tsaki, da kasashen duniya da su hada kai don tabbatar da cewa an kai wa kowane yaro a Najeriya allurar ceton rai.
Hukumar kula da yara ta jaddada mahimmancin karfafa rigakafi na yau da kullun, hada kai da al’umma, da kuma tsarin kiwon lafiya don gujewa barkewar irin wannan annoba a nan gaba.
