Connect with us

Labarai

Nasarawa: Dalibar Kwalejin Da Aka Yi Garkuwa Da Ita Ta Samu ‘Yanci Bayan Biyan Kudin Fansa

 

Wata dalibar kwalejin fasaha ta Isa Mustapha Agwai Polytechnic mallakin jihar Nasarawa, Taye Ajoke da aka yi garkuwa da ita a ranar Litinin din da ta gabata ta samu ‘yanci.

Masu garkuwa da mutane sun sako Ajoke bayan biyan kudin fansa Naira 300,000.

An sace ta ne bayan wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai a lokacin da suke harbe-harbe suka kai hari a gidanta mai lamba Ombi 1 da ke da nisan kilomita biyu daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha, inda suka kai ta inda ba a sani ba.

Lamarin ya yi sanadin jikkata wasu dalibai biyu da wani mai neman gurbin shiga kwalejin.

Da yake zantawa da wakilin Jaridar Punch, Shugaban kungiyar daliban makarantar, Ekom Ayaka, a ranar Alhamis din nan ya ce tun da farko masu garkuwa da Ajoke sun bukaci a biya Naira Miliyan 50 amma daga baya suka rage kudin fansar zuwa Naira 500,000 bayan da suka lura cewa iyalanta da kuma ’yan uwanta sun kaza iya biyan bukatarsu ta farko.

Ya kara da cewa bayan da aka yi ta rokon masu garkuwa da mutane da su kara rage kudin fansa, sun amince su sake ta a kan kudi Naira 300,000.

Ya ce, “Muna godiya ga Allah da ‘yan bindigar da suka sako Ajoke. An sake ta ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba bayan an biya kudin fansa Naira 300,000.

“Masu garkuwa da mutanen da farko sun bukaci Naira miliyan 50 amma daga baya sun rage kudin zuwa Naira 500,000 bayan sun fahimci ‘yan uwa da abokan arziki ba za su iya biyan wannan adadin ba.

“Amma bayan sun yi ta kiraye-kirayen su (masu garkuwa da mutane), sai suka ce wa ‘yan uwanta su biya Naira 300,000 din da ke hannunsu. Haka aka sako ta daga tsarewar da aka yi mata.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet