Siyasa
Zanga-Zanga: Jiga-Jigan Jam’iyyar LP Sun Bukaci INEC Ta Sauke Kwamishinanta
Manyan jiga-jigan jam’iyyar Labour LP, a jihar Imo, a ranar Juma’ar nan, sun mamaye ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, tare da nuna rashin amincewarsu da kwamishinan zaben REC, Sylvia Agu.
Magoya bayan Jam’iyyar ta LP sun bukaci a tsige shi gabanin zaben ranar 11 ga watan Nuwambar 2023 na gwamna da za a yi, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Shugaban LP na jihar, Callistus Ihejiagwa ne ya jagoranci zanga-zangar a ofishin INEC da ke kan titin Owerri-Port Harcourt a Owerri.
Dalilinsu ya ta’allaka ne kan zargin rashin amincewa da yadda kwamishinan zabe na INEC a zaben Majalisar Dokoki ta jiha da ya gabata inda ba a bi hanyoyin gudanar da zaben yadda ya kamata ba. Ya dage cewa hanya daya tilo da za a tabbatar da sahihin zabe a Imo ita ce a tsige REC.
Ya ce: “Hanya daya tilo da za a iya tabbatar da sahihin zaben gwamna a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba ita ce hukumar ta gaggauta sake tura sabon REC a jihar.
“Jam’iyyar ta daina jin dadin REC a halin yanzu a Jihar biyo bayan abin da muka lura a lokacin zabukan ‘yan majalisar dokoki, da kuma zabukan ‘yan majalisun kasa inda ba a bi ka’idojin INEC ba.
“Abin da muke nema abu ne mai sauki, a cire REC kuma ku bi ka’idojin zabe da kuka gindaya. Mun gaji da ‘yan siyasa da ke rike da mukaman shugabanci ta bayan gida, Ya isa ya isa haka.
“Jam’iyyarmu za ta ci gaba da zaman lafiya kuma za ta ci gaba da neman a yi abubuwan da suka dace domin ci gaban Jihar.”
Da yake mayar da martani a madadin hukumar, shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a a ofishin INEC na jihar, Emmanuella Opara, ya ce sun godewa shugabannin jam’iyyar LP da yadda suka gudanar da kansu tare da tabbatar wa jam’iyyar a shirye ta ke na gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Sannan ya kara da cewa hukumar ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen gudanar da sahihin zabe a jihar.
