Siyasa
Kotun Karar Zaben Nasarawa Ta Kori Gwamna Sule Ta Ayyana Dan Takarar PDP
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Nasarawa ta yanke hukunci kan dan takarar jam’iyyar PDP David Umbugadu ne zababben gwamnan jihar.
A hukuncin raba gardama wanda aka yanke da misalin karfe 2:1 kotun mai alkalai mutum uku karkashin jagorancin mai shari’a Ezekiel Ajayi ta yanke tabbatar da Umbugadu a matsayin wanda ya cancanta ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Don haka kotun ta bayar da umarnin janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a baya kuma ta bayar da umarnin a baiwa David Umbugadu.
Za a bayar da ƙarin cikakkun bayanai game da hukuncin a nan gaba.

Pingback: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da ‘Yan Bindiga Sun Harbe Wani Kansila A Katsina - KAKAKI HAUSA