Kasuwanci
PENGASSAN Ta Bayyana Cewa Har Yanzu Gwamnati Tana Biyan Tallafin Man Fetur
Shugaban kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa PENGASSAN, Festus Osifo, ya yi ikirarin cewa har yanzu gwamnatin tarayya na biyan kudin tallafin man fetur.
Osifo, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kwadago ta ‘yan kasuwa, TUC, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a gidan talabijin na Channels a cikin shirin siyasa a yau na ranar Juma’a.
Ya ce saboda tsadar danyen mai a kasuwannin duniya da kuma farashin dala zuwa Naira, har yanzu gwamnati na biyan tallafi.
Osifo ya ce, “Su (gwamnati) suna biyan tallafi a hakikanin gaskiya a yau, akwai tallafi saboda a lokacin da aka tantance farashin farko, farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya kai kusan dala 80 kan ganga guda.
“Amma a yau, ya koma kusan dala 93/94 kan kowace ganga na danyen mai. Don haka, saboda ya karu, sannan kuma farashin [man fetur] ya buƙaci karawa,” in ji shi.
Osifo ya kara da cewa, domin gwamnati ta daina ba da tallafin man fetur, “Dalilin da ya sa farashin ba zai tashi ba shi ne idan kun sami damar tafiyar da canjin ku yadda ya kamata, sannan kuma kuna iya fitar da kayayyaki tare da rage farashin canji.
“Don haka, idan farashin canji ya ragu a yau, ba za mu biya tallafi ba. Amma da farashin canji da farashin danyen mai a kasuwannin duniya, mun bullo da tallafin.
