Connect with us

Kasuwanci

Yadda Aka Samu Karin Farashin Sukari, Fulawa, Da Taliyar BUA Bayan Rage Na Siminti

 

Kwanaki biyu bayan sanar da rage farashin buhun siminti, kamfanin BUA Group a sirrance ya kara farashin kayan abinci, musamman buhunan sukari, da fulawa, da katon na taliya, da wani bincike ya nuna.

Hukumar gudanarwar daya daga cikin katafaren kamfanin siminti a kasar nan a ranar 1 ga watan Oktoba ta sanar da rage farashin siminti zuwa Naira 3,500 kan kowace buhu.

Sai dai sanarwar ta yi matukar fusata da jama’a yayin da dillalan ke fafutukar wayar da kan abokan cinikin cewa rage farashin ya shafi bangarorin da ke sayen kayayyakin kai tsaye daga masana’anta.

Sai dai binciken da wannan jarida ta yi ya nuna cewa kamfanin BUA Foods ya yi shiru ya yin da ya kara farashin sikari, fulawa, da taliya.

KARANTA LABARIN NDLEA Ta Kama Wata Mata Da Wiwi A Filin Jirgin Saman MAKIA

Wakilinmu wanda ya zagaya wasu shaguna a shahararriyar Kasuwar Singa da ke jihar Kano, babbar kasuwa a Arewacin Najeriya, ya lura cewa farashin buhun sukari, gfulawa, da katon din taliya ya karu da N3,500, N2,000 da akalla N1000.

Binciken da jaridar Solacebase ta yi ya nuna cewa, a kwanakin baya an sayar da sikari kan Naira 44,000 kan ko wane buhu, taliya kan naira 8,100 kwali, da buhun fulawa kan Naira 32,500, yanzu haka ana sayar da kayayyakin kan Naira 47,500, N9,000, da kuma N34,500.

Wani dillalin kayayyakin abinci na BUA a Kano ya shaida wa wakilinmu cewa, karin farashin kayayyakin ya biyo bayan rage farashin buhun siminti da kamfanin ya yi.

A cewar dillalin, Yusuf Malami (Ba sunan gaskiya ba) kasancewar ba shi da izinin yin magana, sun lura da karin farashin a wannan makon.

Ya tabbatar da cewa farashin katon na taliyar IRS, da taliyar BUA, yanzu ya koma Naira 9,000 a farashin kamfani, yayin da a kwanan nan aka sayar da shi kan Naira 8,400 kwali, wanda ke nuni da cewa zuwa yanzu zai iya kaiwa N10,000 akan farashin dillalai.

Ya kuma ce “Mun lura da karuwar wannan farashin a makon. Farashin buhun fulawa yanzu ya karu zuwa N34,500 sabanin N31,000 zuwa N32,000 da aka sayar a makon jiya. Kimanin Naira 2,000 aka kara akan buhun fulawar kuma farashin kamfani ne.

”Game da sikari, babu daidaitaccen farashi amma ana sayar da shi har Naira 48,000 yanzu a kasuwa. Naira 44,500 zuwa N45,000 kan kowanne buhu a makon jiya. Wani ya ce min yana sayar da shi akan Naira 46,500 kan kowane buhu.

“Ina kuma so in gaya muku cewa duk waɗannan farashin na kamfani ne,” in ji shi.

Hakazalika binciken da muka gudanar ya nuna cewa tuni farashin kayayyakin ya yi tashin gwauron zabi a gidajen sayar da kayayyaki a cikin birnin Kano.

Wani ma’aikacin kantin sayar da kayan masarufi, Mustapha a Karkasara na karamar hukumar Tarauni, ya shaida wa wakilinmu cewa yana sayar da buhun sukari mai nauyin kilogiram 50 a kan Naira 49,000 bayan ya kai Naira 47,500 a hannun dillalan.

Wani ma’aikacin shago mai suna Ibrahim Musa a karamar hukumar Fagge ya ce ya lura an samu karin farashin sikari da fulawa da kuma taliyar IRS.

A cewarsa, ya sayi buhun sukari mai nauyin kilogiram 50 a kan Naira 48,000, inda ya kara da cewa ya kawo buhun fulawa kan Naira 33,000, yayin da taliyar IRS ya kai Naira 9,100.

Ya koka da cewa duk da karuwar da aka samu, ya tattara bayanan karacin ciniki domin a cewarsa, ya kwashe kusan sati biyu yana sayar da buhun fulawa.

“Ka san babu kudi a hannun mutane. Kafin in sayar da fulawa, wanda aka kawo a lokacin ƙarshe ya ɗauki kusan makonni biyu kafin ta ƙare.

“Muna tattara bayanan yanayin ciniki. Jama’a suna cikin talauci kuma abin dogaro ya yi kadan. Mu dai mun gode wa Allah da addu’ar sa.” Inji Ibrahim.

Abokan ciniki sun kuma nuna rashin jin dadinsu kan karuwar kayayyakin abinci na BUA.

Hajiya Iyami daya daga cikin manyan kwastomomin da ke siyan buhunan fulawa domin yin Gurasa da ake hadawa a cikin gida a Kano, ta koka kan yadda farashin kayayyakin ke ci gaba da tashi.

Ta ce farashin yana tashi kowace rana daga shekaru uku da suka gabata, inda ta tuna cewa farashin ya tashi daga Naira 5,500 kacal kan kowane buhu.

“Abin mamaki, farashin fulawar BUA ya yi tashin gwauron zabo shekaru uku da suka wuce inda buhun fulawar ya kai Naira 5,500 kacal kuma Farashin yana ci gaba da hawa sama.

“Yanzu na sayi buhun fulawa Naira 34,500. Don haka muna kira ga kamfanin BUA da ya rage farashin fulawa kamar yadda muka ji cewa ya rage farashin buhun siminti,” Iyami ta roki.

Kokarin samun kamfanin BUA ya ci tura a matsayinsa na babban dillali a jihar, wanda galibi ya ke magana a madadin kamfanin ya ce ba zai iya magana ba a yanzu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet