Connect with us

Labarai

N20m: EFCC Ta Gurfanar Da Wani Matashi Bisa Zargin Damfarar Matar Sarki Kano

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da wani Umar Bello Sadiq a gaban mai shari’a Zuwaira Yusuf ta babbar kotun jihar Kano bisa zarge-zarge uku da suka hada da almundahana da kuma bayar da cak na jabu.

JaridarSOLACEBASE ta ruwaito cewa an gurfanar da wanda ake tuhuma tare da kamfaninsa, Marula Global Links, bisa zargin karbar kudi naira miliyan 20,000,000 daga hannun Faridah Nasir Bayero, uwargidan Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, don saka hannun jari irin bai daya a cikin kasuwancin ma’adinai.

Sai dai bayan ya karbo kudin, wanda ake tuhumar ya karkatar da kudin don amfanin kansa.

Daya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce: “Kai UMAR BELLO SADIQ DA MARULA GLOBAL LINKS LTD a ranakun 6 ga Mayu 2021 da 25 ga Nuwambar 2021 a Kano da ke karkashin ikon wannan Kotu ka yi rashin amana ta hanyar karkatar da Naira Miliyan 20,000,000 mallakin Faridah Nasir Bayero da ta ba ka da nufin samar da albarkatun masana’antu kuma ta haka kuka aikata laifin da ya saba wa sashi na 308 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashi na 309 na wannan kundi.”

Wanda ake tuhumar ya ki amsa laifinsa lokacin da aka karanta masa tuhumar da ake masa.

Dangane da rokonsa, lauyan masu shigar da kara Sadiq Kurawa ya roki kotun da ta dage zaman shari’ar, yayin da lauya mai kare Shu’aibu Muazu ya mika bukatar neman belin wanda yake karewa.

Mai shari’a Yusuf ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira 500,000 (Naira Dubu Dari Biyar kacal) da kuma wadanda za su tsaya masa guda biyu wadanda dole ne su zama danginsa na jini.

Alkalin ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Nuwambar 2023, domin fara shari’ar.

Share this:
1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Daliban Jami'ar KASU Sun Gudanar Zanga-zanga, Tare Da Barazanar Kauracewa Jarabawa - KAKAKI HAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet