Tsaro
Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da Daliban Jami’ar Da Aka Yi Garkuwa Da Su Guda Hudu
Rundunar sojin kasar nan ta ce a ranar Alhamis ta kubutar da wasu dalibai hudu da suka kammala karatun digiri na biyu a Jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi, wadanda aka yi garkuwa da su ranar Talata daga dakin kwanan su.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da daliban da suka kammala karatunsu ne da sanyin safiyar ranar Talata, inda suka kai farmaki dakinsu da ke Angwan Kaare a cikin karamar hukumar Keffi a jihar inda suka tafi da su inda ba a san ki ina bane.
Amma a ranar Alhamis ne wasu sojojin Najeriya na bataliya ta 117 da ke Keffi suka kubutar da su bayan da suka yi dauki ba dadi da masu garkuwa da mutanen.
Babban kwamandan rundunar, Laftanal Kanal Auwalu Inuwa ne ya bayyana haka ga wakilinmu a Lafiya.
Ya bayyana cewa an kubutar da daliban ne a dajin Angwan Gauta da ke karamar hukumar Keffi bayan kokarin da jami’an sojin suka yi.
Ya ambaci sunayen daliban da aka ceto da suka hada da Rahila Hanya, Josephine Gershon, Rosemary Samuel da Goodness Samuel.
Ya ce za a sake haduwa da daliban ga iyalansu bayan an duba lafiyarsu yadda ya kamata.
