Connect with us

Labarai

An Kama Mutune Shida Da Yunkurin Satar Taragon Jirgin Kasa – ‘Yan Sanda

An kama wasu mutane shida da ake zargi da yunkurin sace taragon jirgin kasa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

A cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Yusufu Mohammed, an kama wadanda ake zargin ne bayan wani rahoto daga mazauna unguwar Bayan kwatas, a shedikwatar tashar jirgin kasa.

Da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels, CP Mohammed ya ce, wani mutum da ya ce shi ma’aikacin kamfanin jiragen kasa ne a jihar Bauchi ya dora tarago biyu a cikin wata tirela da za a kai su Jos amma jami’an ‘yan sanda suka hana su.

KARANTA LABARIN Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Dalibai Biyu A Zamfara

A cewar CP, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa yana aiki ne a kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Filato da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) kan zirga-zirgar jiragen kasa a cikin jihar amma bayan an yi masa tambayoyi an gano wanda ake zargin ya yi karya.

CP ya shaida wa wakilinmu cewa taragon sun nufi garin Jos ne kuma shida daga cikin wadanda aka kama suna hannun hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma ta Najeriya NSCDC a jihar Borno saboda yunkurin kwaso tarago daga Borno.

A halin da ake ciki, NRC ta ce babu wani yunkurin sace wasu taragonta na jiragen kasa a Maiduguri.

Manajan Daraktan NRC, Fidel Okhiria, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Shugaban NRC ya ce sabanin rahotannin da ake yadawa a yanar gizo, ana tura taragon da ma’aikatan da ke cikin faifan bidiyo zuwa Jos da ke Jihar Filato domin yi musu kwaskwarima.

“Hukumar NRC na son fayyace wannan kuskuren rahoton ta hanyar bayyana cewa ana tura taragon a hukumance zuwa NRC Running Shed Jos, a Jihar Filato domin a yi musu kwaskwarima tare da mayar da su don ci gaba da aiki.

“NRC na kokarin tsawaita zirga-zirgar jiragen kasa a duk fadin kasar,” in ji sanarwar a wani bangare.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet