Tsaro
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sake Sace Daliban Jami’ar Tarayya Da Ke Gusau A Zamfara
Wasu ‘yan bindiga a yammacin ranar Asabar sun sake yin garkuwa da wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara.
Daliban biyu, a cewar wani shaidan gani da ido, Namiji da mace ne, wadanda aka yi garkuwa da su a dakin kwanan daliban da ke kusa da jami’ar da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar a unguwar Sabon Garin Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne ‘yan mintoci kadan bayan karfe 8 na dare inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi don tsorata mazauna yankin.
Jami’an tsaro sun yi ta harbin bindiga da dama inda suka yi kokarin fatattakar ‘yan ta’addar amma hakan ta ci tura ‘yan fashin sun tafi da dalibai biyu.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji a halin yanzu suna bin diddigin ‘yan bindigar.
Kokarin yin magana da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Pingback: An Kama Mutune Shida Da Yunkurin Satar Taragon Jirgin Kasa – ‘Yan Sanda - KAKAKI HAUSA