Connect with us

Tsaro

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane Tara Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Daban-Daban

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, a ranar Larabar nan ta yi karin haske dangane da kama wasu mutane tara da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da dillalan miyagun kwayoyi, barayin babur, barayin dabbobi, da barayin shanu.

DSP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana ne hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Ya kara da cewa, an samu nasarar kwato kayayyaki daga wadanda aka kama, da suka hada da kwayoyin maganin D-5 guda 5000, da maganin Tramadol 300, maganin maye 240, baburin sata guda daya, wayoyin lantarki, da almakashi biyu.

Ya kuma ce a wani lamari da ya faru, tawagar ‘yan sintiri a ofishin ‘yan sanda na Maigatari ta kama wani Abubakar Sale da Abdullahi Magaji, wadanda aka same su da wani babur Lifan da ake zargin na sata ne.

Ya kara da cewa binciken da aka yi ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yi jabun takardar babur din.

A cewar kakakin haka zalika, wani sumame da ofishin ‘yan sanda reshen Guri ya kai kauyen Adiyani, an kama Eze Christian da Ibrahim Yusuf.

Ya bayyana cewa, an samu mutanen dauke da adadi mai yawa na magunguna da suka hada da maganin sa maye 240, magani na Tramadol 300, da kuma wasu kwayoyin D-5 5000.

DSP Shiisu ya yi nuni da cewa bincike ya nuna cewa suna kai wa matasa magungunan a karamar hukumar Guri da kewaye.

Haka kuma ya ci gaba da cewa an kama Abdullahi Muazu, Awwalu Uba, Abba Sale, da Jazuli Tukur a kauyen Galadi, a karamar hukumar Maigatari, bisa laifin mallakar wata akuyar da aka yanka da ake zargin ta sata ce.

Ya kara da cewa an kama Abdulrahman Adamu ne da laifin satar wayoyin lantarki a ofisoshi daban-daban a makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gada Kazaure.

Hakazalika ya bayyana cewa an samu wanda ake zargin da yanke wayoyin lantarki da almakashi.

Ya kuma bada tabbacin za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kuliya domin girbar abun da suka shuka.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet