Connect with us

Labarai

Gwamnan Kano Ya Bayyana Jihar A Matsayin Wadda Ta Fi Yaki Da Cin Hanci A Najeriya

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Alhamis din nan ya ce jihar ce kan gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.

Kamfanin dillacin labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa Yusuf ya bayyana haka ne a wajen bude taron kwana guda na yaki da cin hanci da rashawa kan rawar da jami’an tsaro ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tare da rundunar ‘yan sandan jihar ne suka shirya taron bitar a cibiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Dr Abdullahi Baffa Bichi ya wakilta ya ce gwamnatina ba ta tsoma baki a harkokin hukumar.

Ya ce gwamnati mai ci ta gaji dimbin laifukan da ake zargi na cin hanci da rashawa daga gwamnatin da ta shude a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje.

Yusuf ya ce taron zai inganta hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da Hukumar, yana mai cewa, “an yi shi ne don ganin an aiwatar da dokokin hukumar baki daya.”

“A jiya ne wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wani hukunci a kan hukumar. Kotun ta ce hukumar na da hurumin binciken duk wata almundahana da ake zargin a jihar.” Ya kara da cewa.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Muhyi Magaji rimin gado, ya ce makasudin gudanar da taron shi ne inganta hadin gwiwa tsakanin hukumar da jami’an tsaro domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a jihar.

Tun da farko, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Usaini Muhammad Gumel, ya ce rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da baiwa hukumar goyon bayan da ya dace domin karfafa yaki da cin hanci da rashawa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet