Labarai
Gwamna Zullum Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Kayan Abincin Rage Radadi A Borno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zullum, ya sa ido kan rabon tsabar kudi, abinci, da kayayyaki na Naira miliyan 125 ga iyalai sama da 40,000 a karamar hukumar Konduga a wani ci gaba da bada tallafin rage radadi.
Da yake jawabi a garin Konduga a ranar Alhamis yayin da ake gudanar da aikin rabon kayayyakin, wanda ya gudana a cibiyoyi uku (3), Zulum ya bayyana cewa an bada tallafin ne da nufin rage wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta, sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi a watan Mayun bana.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da magidanta maza 15,000, inda kowannen su ya karbi buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da kuma buhun wake 10kg, sai mata 25,000 sun karbi tsabar kudi N5,000.
Zulum ya bayyana cewa, “A ci gaba da kokarin da muke na raba kayan agaji ga marasa galihu a jihar Borno, muna nan a Konduga don rabon kayan ga kimanin mata 25,000 marasa galihu kowacce ta samu tallafi na Naira 5,000, wanda ya kai kusan Naira miliyan 125.
Baya ga wannan, mun kuma raba buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25 da wake buhu 10 kowanne ga magidanta 15,000.”
Zulum ya kaddamar da rabon kayayyakin tallafin don rage radadin cire tallafin man fetir ne a watan Yuli, inda aka fara rabawa kimanin gidaje 300,000 a fadin jihar Borno, ya kuma baiwa al’ummomin da rikicin ya fi shafa.
Daga baya aka fadada rabon zuwa gidaje 400,000.
A kowace mazaba 27 da ke birnin Maiduguri da karamar hukumar Jere, sama da iyalai marasa galihu 2,000 ne suka amfana daga kokarin da Zullum ke yi.
Haka kuma kowane magidanci a yankunan karkara wanda rikici ya shafa zai amfana da rabon.
Baya ga rabon kayan abinci, Zulum ya gabatar da wasu matakai da suka hada da samar da motocin bas guda 80 na jigilar manoma zuwa gonakinsu kyauta, motocin bas 30 na tallafin sufurin ma’aikatan gwamnati da ke zuwa ofisoshinsu, da samar da tallafin motocin bas na birni.
