Connect with us

Featured

Dalilin Da Yasa Ake Sake Kamuwa Da Zazzabin Cizon Sauro Bayan An Warke

Masu iya magana na cewa Lafiya uwar jiki babu mai fi shi da ke.

Rayuwa bata cika daɗi ba idan mutum bashi da cikakkiyar lafiyar da zai yi gwagwarmayar neman halali.

Cutar zazzabin cizon sauro da ake kira da Maleriya na ɗaya daga cikin cutttukan da suka addabi Najeriya kuma aka kasa kawo karshenta.

Najeriya na cikin sahun farko da cutar zazzabin cizon sauro ta fi ƙamari a fadin Duniyar nan ta Buwayi gagara Misali.

Dakta Hussein Abdulkadir, likita ne a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, ya bayyana wa gidan Talabijin na Kakaki cewa cutar Malaria wata kwayar cuta ce da ake kira plasmodium parasite, wadda idan macen sauro ta ciji mutum yake kamuwa da ita.

Dakta Abdulkadir ya ce alamomin cutar maleriya suna farawa ne daga jin zazzabi da kasala da kuma sagewar gabobi da sauransu.

Ya ƙara da cewa hukumar lafiya ta duniya wato WHO, ta bada shawarar yin gwaji kafin tabbatar da cutar zazzabin cizon sauro, domin a san yadda cutar ta ke saboda akwai cututtukan da suke kama da na maleriya a jikin ɗan adam .

Ya kuma bayyana cewa ana warkewa daga cutar maleriya baki daya, matukar sauron bai sake cizon ba.

Acewar Likitan, rashin bin ƙa’idar shan magani kamar yadda aka rubuta, shi ne dalilin da yasa ko da mutum ya warke, zazzabin yake sake dawo masa.

Da yake bayyana yadda al’umma za su guji kamuwa da cutar yace, gujewa cizon shi ne matakin farko da sanya magani da shiga gidan sauro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet