Connect with us

Featured

Yadda Ciwon Apolo Yake Kama Ido Da Hanyar Magancewa Cikin Sauki

Turbar lafiya aka ce a bita da shekara, in ji masu iya salon magana.

Ido wani sashi ne a jikin mutum mai muhimmanci wanda kula da shi yake da mutakar muhimmanci yayin gudanar da rayuwa.

Haka kuma ba karamar tawaya bace ga mutum idan yayi sakacin da ya rasa idonsa a wani tafarkin da ba na Allah ba wato da ganganci.

Ido wata kwaya ce da Allah madaukakin sarki ya sanyawa hallitta domin gani, sai dai ya yi wasu halittun babu ido ba don mai idon yafi wanda bai da shi a wurin Allah ba, sai dai hikima ta Ubangijin halittar.

Afolo guda ne daga cikin ciwukan da suke kama ido, wanda kuma yake janyo kumburi da ja a jikin kwayar idanun da ke dauke da wannan cutar.

Dakta Usaman Mijinwaya Abubakar kwararren Likitan ido ne kuma shugaban kwamitin kula da lafiyar idanu na jihar Kano ya ce ciwon Afolo wani ciwo ne da yake shafar kullutun fatar ido ta ciki, wanda kwayoyin halitta na Virus ke janyo cutar.

Dakta Mijinyawa ya ce ana samun wannan ciwo ne shekara-shekara musamman a lokacin da Damuna tayi nisa, kuma an samu sunan cutar ne daga dawowar jirgin kumbo Afolo da ya je Duniyar wata, wanda aka fara cutar a kasar Ghana.

Ya kuma kara da cewa Afolo ciwo ne mai wuyar sha’ani wanda da zarar kwayar halittar cutar ta shiga mutum to cikin awa 6 za ta fara kama ido guda 1 bayan wasu lokuta sai dayan shima ya kamu.

Da yake bayyanawa gidan talabijin na Kakaki yadda ciwon yake yaduwa Mijinyawa ya ce ba wai da kallon mai ciwon idon bane ake kamuwa ko da ya saka bakin gilas, amma da zarar mai ciwon ya taba idon da hannu ko da tishu kuma ya taba wani abu sannan mutumin da bashi da ciwon shi ma ya zo taba kuma ya shafi fuskarsa shi kenan shima ya zai iya kamuwa da ciwon na Afolo.

Sannan likitan ya ce idan ana so a gujewa yaduwar cutar a cikin al’umma dole ne sai mai dauke da cutar ya kabe kansa na tsahon kwanaki kamar uku, ya daina shiga cikin mutane har sai ya ga likitan ido ya bashi maganin ciwon.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet