Connect with us

Featured

Hadin Gwiwar Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bangar Siyasa Uku, Gabanin Zaben Gwamna A Kogi

Kwanaki kadan kagin a gudanar da zaben gwamna a jihar Kogi wanda aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Nuwamba, rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kashe wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne a garin Anyigba dake gundumar Gabashin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Ovye Aya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talatar nan.

Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun kuma kwato bindigu kirar AK47 guda biyu daga hannun bata garin.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya, jami’an tsaron farin kaya DSS da na hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma (NSCDC) ne suka kai farmakin a wani gini da jam’iyyun siyasa ke tsugunar da ‘yan bangar siyasa.

Sanarwar ta kara da cewa wasu mambobi biyu na tawagar sun samu raunuka harbin bindiga tare da kama mutane bakwai da ake zargi.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A yayin gudanar aiki da nemo mutanen, tawagar ta bayyana kan su ta fuskanci munanan harbin bindiga, inda a martanin da ta mayar an harbe uku daga cikin ‘yan bangar siyasa tare da kwato bindigogin AK47 guda biyu, yayin da ‘yan tawagar biyu suka samu raunukan harbin bindiga da kuma kama mutane bakwai da ake zargi da hannu.

“Don haka, don ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihar, za a ci gaba da kai samame a maboyar da ake zargin masu aikata laifuka da ‘yan daba don hana su zama a mafakar za su gudanar da ayyukansu. Za a ci gaba da gudanar da aikin har bayan zabe”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet