Featured
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Rasuwar Sheikh Yusuf Da Cewa Babban Rashi Ne Ga Al’umma
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin, yana da shekaru 73 a duniya.
Shugaban ya aike da sakon ta’aziyyar ne zuwa ga iyalai, dalibai, da kuma mabiya malamin da ke Kano, da ma Masarautar Gaya.
Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Malamin addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karade muryoyin jama’a a fadin kasar nan, duba da irin dimbin mabiyan da marigayin ke da shi, musamman ma mabiyan darikar Tijjaniyya a ciki da wajen Najeriya .
“A matsayinsa na mai koyarwa, sha’iri, masanin shari’ar musulunci da tsirrai, kuma uwa uba malamin addinin Islama, Sheikh Yusuf Ali ya yi tasiri ga dimbin jama’a a tsawon rayuwarsa wadda ya sadaukar da ita kacokan wajen neman ilimi da yada shi” in ji shugaban.
Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin da kuma gwamnatin jihar Kano da al’ummar jihar da ma daukacin Musulmin Najeriya bisa wannan rashi da aka yi, ya na mai addu’ar Allah ya jikan Malamin.
