Featured
Shugaban Kasa Tinubu Ya Bada Tabbacin Gudanar Da Aikin Qidaya Nan Ba Da Jimawa Ba
Shugaban kasa Bola Tinubu ya baiwa hukumar kidaya ta kasa NPC tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya wajen gudanar da aikin kidayar jama’a a kasar nan.
Shugaban ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Laraba, a wajen taron kaddamar da asusun ajiyar bayanai na kasa, Digital CRVS System da kuma kaddamar da kwamitin kula da CRVS na kasa a fadar shugaban kasa ta Villa dake Abuja.
Yayin da yake kira da a hada kai a tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, Tinubu ya jaddada muhimmancin bayanai ga ci gaban kasa.
Ya yi kira ga kwararrun masu kidayar jama’a da su yi amfani da fasahohin zamani wajen tattara bayanai kan yawan al’ummar Najeriya.
Jaridar Daily Post ta rawaito Tinubu yana mai cewa al’ummar kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen samar da bayanai masu inganci.
Idan zaku iya tuna cewa gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta saki zunzurutun kudi har naira biliyan 200 ga hukumar kidayar ta Kasa NPC domin gudanar da aikin na kidaya.
Yayin da hukumar ta tura kaso mai yawa na kudaden a matakin farko na kidayar jama’a, gwamnatin tarayya ta dage shiri ne saboda wasu dalilai.
