Featured
An Baza Jami’an EFCC Yayin Da Ake Shirin Gudanar Da Zaben Gwamnoni A Bayelsa, Kogi Da Imo
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Kasa EFCC ta tura jami’anta jihohin da za a gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar.
Hukumar EFFC ta tura jami’an ne domin aikin sa ido kan zabe a jihohin Bayelsa, da Kogi da kuma Imo, inda za a gabatar da zaben gwamnoni.
Shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Oyewale ya ce an gudanar da ayyukan ne da nufin duba magudin zabe, sayen kuri’u da kuma laifukan da ke da alaka da su.
Oyewale ya bayyana cewa, “A kokarinta na tabbatar da dakile magudin zabe da laifuffukan da suka shafi kudi.
Za dai a gudanar da zaben gwamnonin ne a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, 2023.
“Ayyukan sa ido na hukumar shi ne magance duk wani nau’i na jawo masu jefa kuri’a ta hanyar sayan kuri’u da sauran magudi a tsarin zabe wanda ya sabawa dokar zabe.”
