Connect with us

Featured

Bayelsa: An Yi Garkuwa Da Jami’in INEC, Sannan Takardun Shigar Da Sakamako Sun Bata

An yi garkuwa da wani jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a karamar hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa.

Masu garkuwa da mutanen sun kama jami’in ta karfi a ranar Juma’a a lokacin da yake jiran ya hau jirgi a mashigin Amassoma Jetty.

“INEC ta kuma bayar da rahoton cewa, jami’in sanya ido SPO (Supervising Polling Officer) da ke aiki a yankin rajista mai lamba 06 (Ossioma) a karamar hukumar Sagbama, an sace shi ne a lokacin da suke jiran shiga jirgi a Amassoma Jetty. An sanar da hukumomin tsaro,” in ji hukumar a wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Juma’ar.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa, A halin da ake ciki, kwale-kwalen da ke jigilar jami’an hukumar 12 domin gudanar da zaben gwamna a jihar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023 shi ma ya kife a ranar Juma’a tare da rasa takardun rubuta sakamakon zaben.

“Muna so mu tabbatar da cewa wani jirgin ruwa dauke da jami’an zabe zuwa yankin rajista-17 (Koluama) a Kudancin karamar hukumar Ijaw ya kife,” in ji mai magana da yawun hukumar a jihar, Wilfred Ifogah.

“Abin farin ciki, ba a rasa rai ba saboda an ceto dukkan jami’an zaben 12 da ma’aikacin jirgin ruwan.

“Duk da haka mun yi asarar takardun shigar da sakamakonmu, na’urar caji da legaje masu ɗauke da tasirin ma’aikata.

“Jimillar wadanda suka yi rajista a yankunan da abin ya shafa sun kai 5,386, sannan adadin PVC da aka tattara ya kai 5,311. INEC na kokarin ganin an gudanar da zabe a yankin da abin ya shafa.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet