Featured
Kaduna: Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Don Kuɓutar Da Ƴan Uwansu Da Aka Tsare
Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa EFCC, ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami’an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato ‘yan uwansu da hukumar ta tsare bisa zargin karya dokar aikin tsaro.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun jami’ain hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, jami’an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke jihar Kaduna.
Za Mu Shigar Da Sabuwar Ƙara Don Ƙalubalantar Hukuncin Da Kotu Ta Yanke – Abba K Yusuf
Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.
A yayin da ake tsare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattaunawa domin warware lamarin.
