Featured
Ƙasashen dake ɗebe Likitocin Najeriya za su fara biyan diyyar Kuɗaɗen da gwamnati ke kashe musu – Ministan Lafiya
Nijeriya ta samar da wani kudiri wanda aka amince da shi a makon da ya gabata wanda ya yi kira ga kasashen da suke dauke mata likitoci su rika biyan diyyar kudaden da gwamnati ta kashe wajen ilmantar da likitocin.
Ministan Lafiya, Dakta Muhammed Ali Pate, ya bayyana haka a shirin BBC Hausa na tattaunawa a tsakanin shugabanni da al’umma kan matsalolin da ke addabar ‘yan kasa mai taken “A Fada A Cika” da aka gudanar ranar Laraba a Abuja.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, yayin da aka tambaye shi wace hanya za a bi domin magance tserewar da likitoci ke yawan yi daga kasar nan zuwa wasu kasashen waje, ministan ya ce akwai matsaloli da dama da suke addabar fannin lafiya da ya kamata su likitocin su yi masu duba na tsanaki tare da sa kishin kasa a ciki.
“Abin da ya dace su likitoci su fara dubawa shi ne, na farko dai ko da mutum ba a makarantar gwamnati ya yi karatu ba to babu makawa gwamnati ta taka rawa a al’amarin da ya shafi iliminsa ta wata fuskar, don haka kamata ya yi su fara duba kishin kasar kafin su yi tunanin barin kasar saboda rashin albashi. Nijeriya kasarmu ce kuma babu wanda zai zo ya gyara mana in ba mu ba.
“Na biyu kuma, su tuna cewa akwa jami’an da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare rayukan ‘yan Nijeriya kuma ake biyan su kudin da bai kai nasu yawa ba, misalin sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro, kuma aikinsu ya fi na likitocin wahala, ka ga wannan ba wani abu ne ba illa kishin kasa, domin albashin nasu ba wani yawa ne da shi ba, wannan kishin kasa ne. Don haka ya kamata kasashen da suke dauke mana likitoci su fara biyan mu kudaden da muka kashe wajen ba su ilimi domin mu samu sukunin maye gurbin wadancan da suka dauke mana. Mun cimma matsaya kan haka a makon da ya gabata kuma za mu gabatar musu da bukatar hakan,” in ji shi.
