Featured
Gwamna Uba Sani ya sha alwashin ɗinke ɓarakar dake tsakanin Gwamnati da al’ummar kudancin Kaduna
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta ɗaura ɗamarar ɗinke duk wata ɓaraka da ke tsakanin gwamnati da al’ummar Kudancin Kaduna.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a sakonsa ga ƙungiyar shugabannin Kiristoci da malaman majami’u, a yayin wani taro da suka gudanar a Majami’ar Throne room da ke garin Kafanchan.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban mataimakinsa na musamman kan harkokin addinin Kiristoci kuma malamin majami’ar Baptist da ke Kaduna, Rabaran Dokta Ishaya Adamu Jangado, ya ce ya tarar da tsamin dangantaka tsakanin al’ummar Kudancin Kaduna da gwamnatocin baya, saboda haka yake son ganin ya dinke ɓarakar.
Uba Sani ya kuma buƙaci haɗin kan jagororin mabiya addinin Kirista, domin ciyar da Jihar Kaduna gaba.
