Featured
Amurka na ƙoƙarin ganin an tsawaita tsagaita wuta a Gaza
Shugaba Biden na Amurka ya ce musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas wani kokari ne nasu na diflomasiyya.
Biden ya ce suna cigaba da matsin lamba domin ganin an sako Amurkawa da sauran mutanen da ake rike da su.
Sannan ya ce zasu cigaba da matsa kaimi wajen ganin yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawaita.
Shugaban na Amurka ya ce abin farin ciki ne ganin yadda ake sada iyalai da ‘yan uwansu da sauran dangi da abokan arziki.
