Featured
Kaduna: Gwamnati za ta yanke hukuncin dandaƙa ga duk wanda aka kama da laifin aikata fyaɗe
Gwamnatin Kaduna ta jaddada matsayinta na yin dandaƙa ga duk namiji ko macen da aka kama ya aikata fyade a jihar.
Kwamishinar Kyautata rayuwa ta jihar, Rabi Salisu, ta ce wannan horo ne domin kawo ƙarshen fyaɗe daga kowane jinsi a jihar.
Rabi Salisu ta ce gwamnatin jihar ta yi dokar dandaƙa ne bayan tuntubar hukumomi da ɓangarorin da abin ya shafa da kuma wayar da kan al’umma kan illolin fyaɗe.
Kwamishinar ta sanar da hakan ne bayan taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatar ta gudanar ranar Alhamis da haɗin gwiwar cibiyar inganta lafiya ta bai-daya (CIHP).
Babban jami’in cibiyar ta CIHP, Dokta Austin Azihaiwe, ya ce taron na da muhimmanci ƙwarai wajen lalubo hanyoyi da dabaru domin samun nasara wajan yaƙi da matsalar cin zarafi a cikin al’umma.
