Featured
Al’umar garin Tudun Biri sun yi ƙarar gwamnatin tarayya kan biyan su diyyar rayukan da aka kashe musu
Al’umar garin Tudun Biri da iftila’in harin bam na sojoji ya afkawa a makon da ya gabata yayin da suke gudanar da taron Maulidin Annabi (SAW), sun kai karar Gwamnatin Tarayya gaban kotu, inda suka nemi a biya diyyar Naira Biliyan 33 a kan rayukan da aka kashe na mutum fiye da 100.
Mutanen sun kai karar ne ta hannun Alhaji Dalhatu Salihu bisa wakilcin lauyansu, Barista Mukhtar Usman, a ranar 8 ga watan Disamba, 2023 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.
Har ila yau, al’ummar garin na neman gwamnati ta nemi afuwarsu a rubuce tare da wallafawa a manyan jaridun kasar nan guda uku.
A cewar masu karar, sun dauki matakin shari’a a kan gwamnati ne domin tabbatar da kare hakkim wadanda suka tsira da kuma wadanda suka rasa danginsu a harin.
A cikin karar, lauyansu ya ce wadanda aka kashe a harin an take musu ‘yancin rayuwa kamar yadda yake kunshe a kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da kuma dokar ‘yancin dan Adam ta Afirka ta shekarar 2010.
