Connect with us

Featured

Kano: Ana zargin ma’aikacin bankin UBA da satar sama da Naira Miliyan 3 daga asusun kwastoma

Wani Matashi mai suna Garzali Wada Ibrahim wanda yake da asusun ajiya a bankin UBA dake Sharaɗa, yace ya kai ƙorafi bankin domin a saita masa manhajar da ake amfani da ita don tura kuɗi, sai ya hadu da wani ma’aikacin banki mai suna Osaka Omada dake bangaren kula da kwastomomi wanda a take ya saita mashi manhajar ta wayar salula wato Mobile Application.

Garzali Ibrahim ya kara da cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2023, an cire wasu Kuɗaɗe daga asusunsa ba tare da izinin sa ba kimanin naira Miliyan uku da dubu dari uku da casa’in (N 3,390,000).
“Bayan an cire ne sai nayi mamaki kuma nayi zargin Osaka Omada na UBA din Sharaɗa ne da yin wannan aika-aikar domin babu wanda yaga lambobin sirrin cire kuɗi daga manhaja ta face Osaka domin yana kallo na saka.” inji Garzali.

Ya cigaba da cewa, kashi na farko na kuɗaɗen da aka sata sun kai kimanin 2,000,000 inda aka tura su zuwa asusun bankin Wema mai lamba 7790847364 mai dauke da sunan BSTPOS-Musa.

Haka zalika kashi na biyu na kudin da aka cire ya kai kimanin 1,300,000 inda aka tura su zuwa asusun Opay mai lamba 9068129712 mai suna Angela Anulika weke.

Ya kuma ce, yayi yunkurin neman haƙƙin sa domin a dawo masa da kuɗaɗen sa amma abin yaci tura. Saboda haka ne ya bukaci Babban Bankin Najeriya ya shiga tsakanin sa da Bakin United Bank Of Africa (UBA) rashen Sharada dake jihar Kano domin a bi masa hakkin zaluntarsa da suka yi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet