Featured
IPMAN ta koka kan matsalolin da ƴaƴanta ke fuskanta daga NNPCL
Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta kasar nan (IPMAN), ta koka game da wasu matsaloli da ‘ya’yanta ke fuskanta wajen samun man da suke sara daga kamfanin mai na ƙasar (NNPCL) su kai gidajen mansu musamman na yankin arewacin ƙasar.
Ƙungiyar ta ce wannan lamarin na iya haifar da ƙarancin man, har da ma rufe gidajen mai da dama.
Mataimakin shugaban ƙungiyar, Zarma Mustapha, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan lokaci man fetur ɗin da suke samu daga NNPCL ba ya kai yawan da suke buƙata.
Zarma ya kara da cewa, wannan ne dalilin da yasa suke siyan mai daga depo-depo masu zaman kansu ,kuma galibi sukan sayi man ne a kan farashi mai tsada wanda yake tasiri kan farashin da suke siyar da man a giajen mansu.
