Featured
Darajar Naira Zata Daga, Yayin Da CBN Ya Waiwayi ‘Yan Kasuwar Canji
Babban Bankin Kasa (CBN) ya fara sayar da dala ga ‘yan kasuwar canji kudade a Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talatar nan, ta hannun Dr Hassan Mahmud, Daraktan Sashen Ciniki da Musaya na CBN.

A cewar babban bankin, za a rika bayar da $20,000 ga kowane ma’aikacin canjin kudi da ya cancanta a duk faɗin ƙasar.
Za a siyar da wannan jimilla ga kowane dan canji akan kudi Naira 1,301 kan dala 1, wanda ke wakiltar mafi karancin adadin kudaden da aka kashe a kasuwar musayar kudaden waje ta Najeriya (NAFEM) kamar yadda aka yi a cinikin da ya gabata.
Ya ce duk dan canji an yarda ya sayar wa masu amfani da dalar a wani mataki da bai wuce kashi ɗaya cikin ɗari ba, sama da adadin sayan da aka yi daga CBN.
