Featured
An Samu Bullar Cutar Sankarau A Wasu Makarantun Kwana Da Ke Jihar Yobe
Wasu Rahotanni daga jihar Yobe na bayyana cewa an samu bullar cutar Sankarau a wasu makarantun kwana, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar akalla dalibai 20.
Wasu Majiyoyi sun ce an samu bullar cutar ne a makarantun kwana guda uku da ke kananan hukumomin Potiskum, Fika da Fune na jihar, wadanda suka hadar da ta mata biyu da ta maza guda daya.
Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Ilimi Dr. Muhammad Sani Idris yayin tabbatar da bullar cutar, ya ce a yanzu haka sauran daliban da suka kamu da ita na karbar magani a asibitin kwararru na jihar da ke Potiskum.
RFI ta rawaito cewa gwamnatin ta ce ta na aiki tukuru domin dakile yaduwar wannan cuta a makarantun da ta bulla da ma fadin jihar.
