Featured
Dalilan Da Suka Sa Tattalin Arzikin Najeriya Ya Shiga Tasko
Najeriya kasa ce da ke amsa sunan jagora a Afrika sai dai a halin yanzu kasar na fuskantar taɓarɓarewar tattalin arziƙi mafi muni wanda ke haifar da wahalhalu sannan kuma yake fusata al’ummar ƙasar.
Ƙungiyar ƙwadago ta Kasa NLC, ta shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar ta kwana biyu wadda ta fara a jiya, inda ta buƙaci gwamnati ta ƙara ɗaukar matakai, sai dai a daren jiya Talata ta dakatar da zanga-zangar.
A yanzu adadin kuɗin litar man fetur ya karu fiye da sau uku, wanda ya ninka yadda ya ke a watanni tara da suka wuce, yayin da farashin kayan abinci kamar shinkafa ya rubanya fiye da ninki biyu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Sai kuma faduwar darajar Naira, wanda Dala 1 sai da ta kai sama da Naira 1500, a gwamnatance, yayin da a kasuwanin bayan fage kuwa ta haura 1800.
Haka kuma a wata hira da gidan Talabijin na Kakaki ya yi da Dakta Abdulsalam Muhammad Kani, wani masanin tattalin arziki, ya ce sai kasar nan ta koma samarwa da fitar da mafi yawan kayan da ake shigo mata da shi daga kasashen waje, idan ana son gyara matsalar da ake fuskanta.
Waɗannan abubuwa guda uku sun nuna irin matsalolin da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta gashi kuma albashi bai yi daidai da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ba.
