Connect with us

Labarai

Sheikh Gumi Ya Bukaci Shiga Tsakanin ‘Yan Bindiga Da Gwamnati Don Kubutar Da Daliban Kuriga

Fitaccen malamin addinin Isulunci a Kasar nan Sheikh Ahmad Gumi ya gamu da kakkausar suka daga daidaikun al’ummar kasar musamman a mabanbantan dandalin sada zumunta ciki har da Twitter ko kuma X bayan tayin da ya mika na shiga tsakani don ceto daliban Firamare da Sakandiren garin Kuriga 287 wadanda ‘yan bindiga suka sace a makon jiya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, ‘yan bindiga suka farwa makarantar Firamare da Sakandiren garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna tare da sace dalibai 287.

Wata sanarwa da ofishin Gumi ya fitar ta bayyana aniyar malamin ta ganin ya taimaka wajen tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga a kokarin kubutar da tarin daliban.

Sanarwar ta Gumi ta ce akwai bukatar gwamnatin ta yi amfani da salon da ta yi wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna da ‘yan bindiga suka sace cikin watan Maris din 2022.

Ka zalika Sheikh Gumi ya bukaci shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kaucewa makamancin kuskuren da magabacinsa Muhammadu Buhari ya yi wajen kin amincewa da tattaunawa tsakaninsa da ‘yan bindigar.

Sanarwar ta ruwaito Gumi na cewa a shirye ya ke ya siga tattaunawar fahimtar juna don samun damar kubutar da daliban na Kuriga.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet