Connect with us

Featured

Shugaban Kasa Tinubu Ya Hana Biyan Kudin Fansa

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci jami’an tsaro da kada su kuskura su biya kuɗin fansa don a saki kusan ɗalibai 300 da malaminsu da aka yi garkuwa da su makon da ya gabata daga wata makaranta da ke Kaduna.

Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar an kuɓutar da duk mutanen da aka sace ba tare da biyan ƴan bindigar kuɗin fansa ba.

Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ne ya shaida wa ƴanjarida umarnin na shugaban Kasa a ranar Laraba.

Ministan ya ce shugaba Tinubu ya faɗa wa sojojin da ke laluben inda ɗaliban suke su tabbatar “ba a biya ko sisin kwabo ba”.

Tun farko, ƴan’uwan ɗaliban da aka sace sun ce ƴanbindiga sun buƙaci a biya su kuɗi mai yawa domin su saki yaran da suka sace daga makarantarsu a ƙauyen Kuriga.

Cikin makon da ya gabata, an sace mutane da dama ciki har da fiye da mutum 60 daga wani ƙauye a dai jihar ta Kaduna.

Cikin shekara uku da ta gabata, ɗaruruwan ɗalibai aka sace. Wasu a cikinsu an sake su bayan tattaunawa da hukumomi duk da cewa jami’ai sun musanta biyan kuɗin fansa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet