Connect with us

Featured

An Bukaci Gwamnan Kano Da Ya Nada Murja Kunya A Matsayin Mai Bashi Shawara

Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya nada ‘yar TikTok din nan da ake ta cece-kuce akanta, Murja Ibrahim Kunya a matsayin babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin kafafen sadarwa na zamani.

Sheikh Khalil ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata a cikin wani shirin gidan rediyon Freedom.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa, Murja Ibrahim Kunya, ta dade tana fafatawa da hukumar Hisbah ta jihar Kano inda ta zarge ta da rashin da’a a cikin ayyukanta da sauran su.

A kwanakin baya ne wata kotun shari’ar Musulunci a Kano karkashin jagorancin Nura Yusuf Ahmad ta bayar da umarnin cewa ayi wa ‘yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya gwajin tabin hankali a wani asibitin gwamnati domin sanin halin da kwakwalwarta ke ciki.

Mai shari’ar ya bayyana cewa a lokacin da ta bayyana a kotu a baya, da alama ba ta cikin hankali saboda zargin da ake yi mata na shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Hukumar Hisbah ta jihar a ranar 13 ga watan Fabrairu ta kama Kunya, mai shekaru 26, tare da gurfanar da ita a gaban kotun shari’a, bayan da ta zarge ta da laifin yin tada hankalin jama’a, da rashin da’a, da yunkurin daukar ‘yan mata karuwanci bisa kiran kanta da shugabar Karuwai kuma shugabar ‘yan kwalta.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet