Featured
Ina Magana Da Shugaban Kasa Kullum Kan Matsalar Tsaro — Gwamnan Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ce a kullum sai ya yi magana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sau biyu kan matsalar tsaron jihar.
Uba Sani ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV.
Kakaki24 ta rawaito a ranar 8 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki makarantar firamare da karamar sakandare da ke Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 300 da wani shugaban makarantar Abubakar Isah da rana tsaka.
Sannan A daren Lahadin da ta gabata kuma wasu ‘yan bindigar suka sake yin garkuwa da akalla mutane 87 a kauyukan Tantatu da Aguba da ke gundumar Kufana a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
A yayin hirar gwamnan na Kaduna ya bayyana cewa Tinubu da hafsoshin tsaro sun dukufa wajen kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Uba Sani ya kara da cewa gwamnatin sa ta bullo da wani shiri domin taimakawa al’ummar jihar ta hanyar tallafawa ‘yan kasuwa da magidanta.
