Connect with us

Featured

Wata Gobara Ta Kone Wasu Shaguna 40 A Kasuwar Zawaciki Da Ke Kano

Wata gobara ta kone shaguna kusan shaguna 40 a kasuwar Zawaciki da ke kusa da gidaje sama da 1000 a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Wani shaidan Gani da idonmai suna Ahmad Nasir Wali ya ce gobarar ta tashi ne a Larabar da ta gabata kuma ta dauki awanni da dama kafin hukumar kashe gobara ta jihar ta iya kashe gobarar.

Ya ce an rasa kayayyakin abinci, siminti, katako, da shagon POS, da dai sauran kadarori da kayayyaki na miliyoyin naira.

Wasu mazauna yankin sun ce jami’an kashe gobara daga wani kamfani mai zaman kansa mai suna Mamuda Group ne suka fara isa wurin domin taimakawa wajen shawo kan lamarin.

Da aka tuntubi kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu kira daga wani mazaunin unguwar Malam Muhammad Baba, da misalin karfe 12:37 na safe, inda nan take suka umurci cibiyoyin su na Sharada da Audu Bako da su tashi don kai dauki da sauri zuwa wurin.

Yusuf ya ce daga baya an aike da wata mota daga shedikwatar kuma sun yi nasarar kashe gobarar.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, Aminu Isa, ya ce ya zo wurin ne da misalin karfe 1 na ranar Laraba bayan da aka yi masa waya cewa wuta ta kama shagon.

Ya ce, ”Da isowa na, na gane na rasa komai a shagon da wuta ta lalata.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet