Featured
Ku Daina Tsinewa Najeriya – Tinubu Ga Shugabannin Addinai Da Malamai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bukaci malamai da jagororin addinai su daina tsinewa najeriya a tarukan su ko wajen wa’azin su.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin buda baki da malaman Addini da masu sarautun gargajiya a fadar sa.
“Wannan itace kasar ku, zargin shugaba wannan ba laifi bane, in kunso zaku iya sauya shi idan zabe yazo, amma tsinewa kasa ko la’antar ta wannan ba dai dai bane” inji shi.
A karshe Tinubu ya bukaci malamai da shugabannin addinai su kasance masu adalchi wajen sukar masu riƙe da madafun iko.
