Connect with us

Featured

Gwamnatin Kano ta kori ma’aikatan lafiya 3 bisa karbar kudin da suka wuce ƙima a hannun marasa lafiya

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar wasu ma’aikata tare da dakatar da wasu ma’aikatan na babban asibitin Karamar hukumar Kabo nan take, bayan samunsu da laifin cazar kudade daga marasa lafiya da suka wuce ƙima.

Shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda ne, ya bayyana hakan jim kadan bayan sanya hannu kan amincewar da hukumar ta gabatar bayan kammala ziyarar da sukayi.

Kakaki 24, ta ruwaito cewa Asibitin wanda babban sakataren hukumar da babban darakta na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano (KNCDC) Dr. Muhammad Abbas, da darakta janar na CSACA Dr. Usman Bashir suka ziyarce su, sun nuna bacin ransu ga abinda ya faru tare da amincewar daukar matakin gaggawa.

Dakta Nagoda ya bayyana cewa an kama jami’ai 3 na sashen X-ray suna cajin marasa lafiya dubu 12,000 na gwajin X-ray maimakon farashin asibiti da aka amince da shi na dubu 2,000, kuma babu wata takarda da za ta nuna a matsayin shaidar biyan kuɗin da ke barin wurin don aiwatar da gwajin, lamarin da yasa ake X-ray 10 kacal a kowanne mako duk da cewa Injinan Asibitin na X-ray 2 suna aiki.

Daga nan sai ya amince da korar jami’an 3 nan take.

Har ila yau, shugaban hukumar ya amince da dakatar da akawun Asibitin da mai binciken kudi da shugaban dakin gwaje-gwaje saboda sayar da kayan gwajin cuta mai karya garkuwar jikin dan Adam wanda kyauta gwamnatin jihar ta ba wa cibiyoyi, kuma an umarce su da su kai kansu ga hedikwatar hukumar don ci gaba da ladabtar da su.

Bugu da kari, Dakta Nagoda ya bayyana cewa dakin karbar Haihuwa na Asibitin ba shi da tsari domin ba shimfidar gado a kan gadaje, babu wani jami’in kula da gurin, haka kuma an wulakantar da wasu kayayyakin kula da lafiyar al’umma, wanda wani dan majalisa ya bayar da gudummawarsu shekaru 4 da suka gabata, tare da nuna halin ko in kula da kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Shugaban ya kuma ce abin bakin ciki ne bayan mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ya dawo da kowane ma’aikacin lafiya a kan ma’aunin albashin CONHESS, amma duk da haka suna cin zalin Marasa Lafiya.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta aike wa manema labarai a Kano ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su rika gudanar da ayyukansu don cigaba da kula da lafiyar al’ummar Kano.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet