Featured
Bauchi: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Matashi Kan Zargin Hallaka Dan Uwansa
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani matashi Mai suna Isyaku Babale mai shekaru 30 a unguwar Anguwan Dawaki da ke cikin birnin Bauchi bisa zarginsa da daba wa dan uwansa wuka har ya rasa ransa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Bauchi.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da jami’an ‘yan sanda reshen ofishin ‘yan sanda na garin Bauchi ya samu, kuma an tura jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru nan take.
“Sun garzaya da wanda abin ya shafa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.
“Wannan lamari ya sa jami’an tsaro suka fara farautar wanda ake zargin, kuma aka kama shi a kusa da unguwar Kasuwan Shanu a cikin babban birnin Bauchi.
“Binciken farko da ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wuka ya daba wa kaninsa a ranar 31 ga watan Maris, 2024 da misalin karfe 04:00 bayan wata takaddama a tsakaninsu,” inji shi.
Kakakin yan sandan ya kara da cewa rikicin ya fara ne a lokacin da kanin (wanda ake zargin) ya bukaci kanin nasa (wanda aka kashe) ya daina shan ‘sholi’ a dakinsu.
“Dukkansu biyu suka fusata juna, suka fara faɗa. Jim kadan da sasantawa, wanda ake zargin ya gudu ya dauko wani abu mai kaifi, wanda ake zargin wuka ce, ya daba wa wanda aka kashe a ciki.
“Bincike ya nuna cewa a ko da yaushe mutanen biyu suna fada da juna tare da amfani da makamai,” in ji shi.
Jaridar Punch ta rawaito cewa SP Wakil ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin domin bankado wasu dalilan da suka sa wanda ake zargin ya aikata laifin kafin a gurfanar da shi gaban kuliya.
